Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kara dage wa kananan sana'o'i haraji zuwa shekaru 4 masu zuwa
2020-04-27 11:00:32        cri
A jiya Lahadi ne kasar Sin ta bayyana sake dagewa kananan sana'o'i dake cikin kasar haraji zuwa shekaru 4 masu zuwa, a wani mataki na kara kyautata hidimomin kudi ga wannan rukuni.

Tsarin sauwake haraji na baya da aka aiwatar, wanda aka tsara karewar sa a shekarar da ta gabata, a yanzu an kara shi zuwa ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2023, kamar yadda wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kudi da ta tattara harajin kasar suka fitar.

Sanarwar ta kara da cewa, an dauki matakin ne domin tallafawa manufa, da karfafa gwiwar cibiyoyin hada hadar kudi, wajen samar da hidimomin kudi ga kananan sana'o'in. Tun a shekarar 2017 ne dai mahukuntan kasar suka ayyana janye harajin VAT ga hukumomi kudin kasar, bisa hada hadar da suka yi ta samar da basussuka masu ruwa ga kanana, da masu jari kankane, da ma sana'o'in da daidaikun mutane ke gudanarwa.

Sanarwar hadin gwiwar ta kuma ce harajin VAT, wanda irin wadancan rukuni na masu sana'o'i suka riga suka biya, za a cire musu a watanni dake tafe, ko a mayar musu da kudaden su kai tsaye. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China