Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tsame mutane miliyan 9.47 daga kangin fatara zuwa watan Maris
2020-04-24 11:26:10        cri
Gwamnatin Sin ta kammala aikin ginin gidaje sama da miliyan 2.66 domin tsugunar da mutane miliyan 9.47 a shirin kasar na yaki da fatara ya zuwa karshen watan Maris, kawo yanzu kashi 99% na mutanen sun riga sun shiga gidajen, a cewar kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin (NDRC) jiya Alhamis.

NDRC ya ce, daga cikin kashi 89 bisa 100 na mutanen da suka shiga gidajen wadanda za su iya yin aiki, a kalla mutum guda daga cikin ko wane gida ya samu aikin yi.

Ya zuwa tsakiyar watan Afrilu, an dawo bakin irin wadannan manyan ayyukan guda 132 na gina makarantu da asibitoci bayan da aka samu ci gaba a yaki da annobar COVID-19.

Kwamitin NDRC zai ci gaba da bin diddigi domin tabbatar da mutanen da aka baiwa gidajen sun samu ayyukan dogaro da kai kana da bunkasa harkokin kasuwanci don tabbatar suna samun karin kudaden shiga.

A kokarin gwamnatin na tabbatar da ganin an kawar da talauci a shekarar 2020, kasar Sin tana aikin sake tsugunar da matalauta kusan miliyan 10 zuwa wasu wuraren da suka fi dace da rayuwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China