Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a yi kokarin gudanar da ayyuka 6 da ba da tabbaci ga ayyuka 6
2020-04-24 11:33:37        cri

Kwanakin baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyara lardin Shaanxi, inda ya nanata cewa, ya kamata a yi kokarin gudanar da ayyuka 6 da ba da tabbaci ga ayyuka 6, don kawar da illar da cutar COVID-19 ke jawowa, da kuma tabbatar da cimma muradun kawar da kangin talauci a duk kasar, da kafa al'umma mai wadata a duk fannoni.

Ba da tabbaci ga ayyuka 6 sun hada da tabbatar da samar da guraben aikin yi, ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, da tallafin kamfanoni a kasuwa, har ma da samar da isasshen hatsi, da tabbatar da tsarin masana'antu da tsarin samar da kaya, da kuma tabbatar da ayyukan gwamnatocin wurare wurare daban-daban. Kazalika, tabbatar da ayyuka 6 sun hadda da tabbatar da samar da cikakkun guraben aikin yi, da tabbatar da kasuwar hada-hadar kudi da cinikayyar waje da shigo da kudaden ketare da zuba jari da kuma tabbatar da hasashen da aka yi kan tattalin arzikin kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China