Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan kiwon lafiyar Najeriya ya halarci taron musayar fasahohin yaki da cutar COVID-19 a tsakanin Sin da Afirka ta yanar gizo
2020-04-28 12:03:22        cri

A jiya ne, aka gudanar da taron farko na musayar fasahohin yaki da cutar COVID-19 a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta yanar gizo, a manyan biranen Sin da kasashen Afirka fiye da 20, inda ministan kiwon lafiyar kasar Najeriya Osagie Ehanire, da sauran jami'an gwamnatin kasar, da jami'an cibiyar yaki da cututtuka ta kasar suka halarci taron.

A yayin taron, direktan kula da horar da kwararru masu yaki da cututtuka masu yaduwa na cibiyar yaki da cututtuka ta kasar Sin Ma Huilai, da kuma babban masanin yaki da cututtuka masu yaduwa na kasar Sin forfesa Wu Zunyou, da sauran masana sun yi musayar ra'ayoyi tare da bangaren Afirka kan ayyukan shawo kan cutar.

Minista Ehanire ya bayyana godiya ga gwamnatin kasar Sin, bisa kafa dandalin mu'amalar fasahohi a tsakaninta da kasashen Afirka. Kana ya bayyana cewa, fasahohin yaki da cutar COVID-19 suna da amfani sosai, kuma Najeriya za ta koyi fasahohi bisa yanayin da take ciki, tare da da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, don kawo karshen cutar cikin gaggawa. Ya ce Najeriya ta yi musayar ra'ayoyi tare da masanan Sin kan yadda za a dinga bibbiyar mutanen da suka kamu da cutar ta fasahohin zamani, da ayyukan kandagarkin cutar a na'urorin hawa bene na lift, da dai sauransu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China