Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka sun hada kai don yakar COVID-19 don samar da kyakkyawar makoma ga alummun Sin da Afirka
2020-04-24 15:38:33        cri
Yanzu haka cutar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa a nahiyar Afirka, tare da haifar da mummunan tasiri a nahiyar, mai raunin tsarin kiwon lafiya. A 'yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin ta ci gaba da taimakawa kasashen nahiyar ta fannoni daban-daban.

A ranakun 21 da 22 ga wata agogon wurin, tawagar ma'aikatan lafiya da kasar Sin ta turo Burkina Faso, sun yi musayar horaswa na musamman da ma'aikatar lafiyar kasar, kan matakan kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19.

A ranar 22 ga wata da rana, likitoci da dama da suka yi jinyar marasa lafiya da suka kamu da COVID-19 a Wuhan na kasar Sin, sun raba fasahohinsu ga shugabannin wasu asibitoci da ake kebe don jinyar masu fama da cutar COVID-19 a Zimbabwe, ta kafar bidiyo, kan fannonin jinyar marasa lafiya.

Kana a ranar 22 ga wata agogon wurin, an shirya bikin mika gudummawar kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Togo, wanda ya gudana a ma'aikatar lafiyar kasar.

Haka kuma, a wannan rana, an shirya makamancin wannan biki na mika gudummawar kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin gami da kamfannonin kasar suka baiwa kasar Senegal, bikin da ya gudana a Dakar, babban birnin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China