2020-04-24 09:46:28 cri |
Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, shi ne ya jagoranci bikin mika gudummowar kayayyakin lafiyar ga shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a fadar shugaban kasar.
Kayayyakin sun hada da takunkumin rufe fuska 166,000, da rigunan baiwa jami'an lafiya kariya 7,600, da kayayyakin gwaje gwaje 20,000, sai safar hannu 12,000, da kuma na'urorin taimakawa numfashi guda biyar. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China