Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu rahoton adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da COVID-19 a rana guda a Nijeriya
2020-04-22 13:19:41        cri
An tabbatar da samun sabbin mutane 117 da suka kamu da cutar COVID-19 cikin sa'o'i 24 a Nijeriya, adadin da ya zama mafi yawa da aka samu a rana guda, tun bayan samun bullar cutar a ranar 27 ga watan Fabreru, a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Nijeriya (NCDC) ta ce zuwa karfe 11:25 na daren jiya agogon kasar, jimilar mutane 782 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, tana mai cewa an sallami mutane 197 bayan sun wake daga cutar, yayin da wasu 25 suka mutu sanadin cutar, a fadin kasar.

Kawo yanzu, annobar ta bazu zuwa jihohin kasar 24 da birnin tarayya Abuja.

Darakta Janar na cibiyar NCDC Chikwe Ihekweazu, ya yi gargadin cewa, cutar na iya shiga dukkan jihohin kasar.

Tun bayan barkewar cutar a Nijeriya, gwamnati ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen kasar, sannan ta rufe dukkan makarantu tare da kulle birnin Abuja da jihohin Lagos da Ogun, baya ga daukar wasu tarin matakai da nufin dakile yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China