Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyun Afirka da kusoshin siyasan Afirka sun bayyana kyakkyawar dangantakar Sin da Afrika wajen yaki da annobar COVID-19
2020-04-24 15:50:48        cri
Shugabannin kasashen Afrika da jami'iyyun siyasa na Afirka sun aike da wasiku ga sashen hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda suka yi matukar yabo game da matakan da Sin take dauka a zahiri wajen tallafawa kasashen Afrika a yaki da cutar COVID-19. Haka zalika sun yabawa aniyar gwamnatin Sin wajen kare lafiya da hakkokin jama'ar kasashen Afrika dake kasar Sin. Sun yi amanna cewa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika za ta dore duk wuya duk rintsi, kuma Sin da Afrika za su gina tsarin hadin gwiwa na kut-da-kut don samar da kyakkyawar makoma ga dukkan al'umma ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika na yaki da annobar COVID-19. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China