Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu za ta kawar da maleriya yayin da take yaki da COVID-19
2020-04-26 16:48:23        cri
A yayin da ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin maleriya ta kasa da kasa a ranar Asabar, gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta sanar cewa za ta kawar da cutar duk da yakin da kasar ke yi da annobar COVID-19.

Ana gudanar da bikin ranar yaki da zazzabin malariya na duniya a ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara domin nazartar matakan da kasa da kasa ke dauka game da batun yaki da cutar maleriyar.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi shirin kawar da zazzabin maleriya daga doron kasa nan da shekarar 2030.

Ministan lafiyar kasar Afrika ta kudu Zweli Mkhize ya ce adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Afrika ta kudu ya kai 4,362, yayin da mutane 86 suka mutu, ya zuwa ranar Asabar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China