Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: Ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin Sin wajen yaki da cutar COVID-19
2020-04-27 13:29:38        cri

Jiya Lahadi, shehun malami a fannin siyasa da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na jami'ar Abuja ta kasar Nijeriya Agaba Halidu ya fidda sharhi mai taken "Sin na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 cikin himma da kwazo: Mene ne kasashen Afirka za su iya koya daga wajenta?" a jaridar Leadership ta kasar Nijeirya. Cikin sharhin, ya yabawa kasar Sin kan yadda take sa kaimi ga al'ummomin kasarta, ya kuma jaddada cewa, sabo da matakan kandagarki da hana yaduwar annobar da kasar Sin ta dauka yadda ya kamata, sauran kasashen duniya za su iya samun lokacin tanadin ayyukan yaki da annobar, shi ya sa, ya yi kira ga kasashen Afirka da su koyi fasahohin kasar Sin, da kuma yin hadin gwiwa domin cimma nasarar yaki da cutar cikin sauri.

Ya kuma kara da cewa, dukkanin al'ummomin kasar Sin sun cimma matsayi daya da kuma yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce, yadda kasar Sin ta gina asibitoci masu inganci guda biyu cikin kwanaki 10, da kuma sa kaimi ga al'ummomin kasar da su ba da taimako ga birnin Wuhan ya burge shi kwarai da gaske. Kuma dukkanin jita-jitar da aka yi kan sakamakon da kasar Sin ta cimma wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ba su da tushe. A cewarsa ya dace kasashen Afirka su koyi fasahohin kasar Sin, da kyautata ayyukan gina ababen more rayuwa, da habaka ayyukan kimiyya da fasaha domin ci gaba da karfafa ayyukanta na fuskantar kalubaloli. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China