Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci jamiai da su kasance masu kiyaye muhallin tsaunukan Qinling
2020-04-21 11:33:45        cri

Shugban kasar Sin, kana babban sakataren Kwamitin koli na jam'iyyar JKS Xi Jinping, ya bukaci jami'an lardin Shaanxi dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, da su kasance masu kiyaye yanayin muhallin tsaunin Qinling.

Xi ya yi wannan kira ne, yayin da ya ziyarci yankin kare muhalli na Niubeiliang, don ganin yadda ake aikin kare muhalli a tsaunin Qinling.

Ya ce, yadda aka gina gine-gine ba bisa ka'iba a tsaunin na Qinling a baya, wani babban darasi ne. Kuma daga yanzu, ya kamata duk wani jami'i dake aiki a lardin Shaanxi ya koyi darasi, a guji aikata kuskuren da ya faru a baya, kana su yi aiki a matsayin masu kiyaye muhallin tsaunin na Qinling.

Xi ya ce, a matsayinsa na iyakar kasar ta arewa da kudu, tsaunin Qinling cike yake da itatuwa daban-daban da namun daji ba ko'ina ake samun su ba kamar manyan Panda, da birrai masu launin zinare da kuma shamuwa ko Ibis.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China