Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yabawa rawar da kasuwanci ta intanet ke takawa wajen rage fatara da raya karkara
2020-04-21 11:49:52        cri

Sakatare Janar na kwamitin koli na JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana kasuwanci ta intanet a matsayin kasuwanci mai dimbin damarmaki dake kara yin fice. A cewarsa, zai bunkasa cinikin amfanin gona da taimakawa mazauna karkara yaki da fatara da kuma inganta raya yankunansu.

Shugaba Xi Jinping, ya bayyana haka ne da yake jawabi yayin rangadin da ya kai kauyen Jinmu na Yankin Zhashui dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin.

A shekarun baya-bayan nan, kauyen dake yankin tsaunukan Qinling, ya yaki talauci ta hanyar kirkiro sana'ar samar da nau'in bakin laimar kwado.

Shugaban ya kuma tattauna da mazauna kauyen a cibiyar horo ta kauyen, lokacin da suke shirye-shiryen gudanar da wani shirin kai tsaye ta intanet, domin tallata amfaninsu na gona. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China