Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya isar da gaisuwa ga masana kimiyan da suka harba tauraron dan-Adam na Dongfanghong-1
2020-04-24 11:30:20        cri
Jiya ne shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya amsa wasikar da tsoffin masana kimiyan da suka yi aikin harba tauraron dan-Adam na Dongfanghong-1, suka rubuta masa, yayin da kasar ke shirin bikin cika shekaru 50 da nasarar harba tauraron dan-Adam na farko da ta kera.

A cikin wasikar, Xi ya mika musu sahihiyar gaisuwa tare da fatan ma'aikatan sama jannatin, za su hanzarta raya masana'antun sarrafa kayayyakin sararin samaniya mai karfin gaske.

A ranar 24 ga watan Afrilu ne, kasar Sin ta ke bikin wannan rana, wanda ya zo dai-dai da ranar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin karo na biyar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China