Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi rangadin aiki a Xi an
2020-04-23 09:58:17        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai rangadin aiki a birnin Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi jiya Laraba, inda ya ziyarci kamfanin kera motoci na Shaanxi, da jami'ar Jiaotong ta Xi'an, da wani titin kasuwanci, a kokarin kara sanin yadda ake komawa bakin aiki da kuma maido da zaman rayuwar yau da kullum a wurin.

Kamfanin kera motoci na Shaanxi, shi ne kamfanin kera motoci mafi girma a arewa maso yammacin kasar Sin. Kamfanin dake gaban wajen kera motoci masu amfani da makamashi maras gurba muhalli, sabbin makamashi da sauran sabbin motoci na zamani. Kamfanin yana da fasahohi fiye da 220. A ranar 14 ga watan Febrairun bana, kamfanin ya koma bakin aiki kamar yadda ya saba.

A daren ranar 22 ga wata, Xi Jinping ya ziyarci wani titin kasuwanci a Xi'an. Sai dai tun barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ya sa babu mutane a titin na kasuwar dare, amma yanzu harkokin sun fara bunkasa a titin. Xi Jinping ya kewaya titin don ganin yadda ake kokarin maido da kasuwanci a titin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China