An yi taron tattauna batun zurfafa gyare-gyare a kasar Sin
Shugaban kasar Sin, jagorantar aikin zurfafa gyare-gyare na kasar, mista Xi Jinping, ya kira wani taro na kwamitin tsakiyar kasar Sin mai kula da aikin zurfafa gyare-gyare a kasar daga dukkan fannoni a yau Litinin. Inda shugaban ya jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da kokarin kyautata tsare-tsaren kasar, musamman ma a fannin raya kasa. Sa'an nan a yi amfani da fifikon da ake da shi a fannin tsarin siyasa don tinkarar barazana daban daban. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba