Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Da Afirka Suna Hadin Gwiwa Domin Yaki Da Cutar COVID-19
2020-04-27 13:38:46        cri

A halin yanzu, kasashen Afirka na fama da matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Cikin 'yan kwanakin nan, kasashen Kenya, Uganda, Sudan ta Kudu, Benin, da kuma Angola da sauransu, sun karfafa matakan kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

A matsayin 'yan uwa na kasashen Afirka, kasar Sin tana ba da taimako gare su ta hanyoyi daban daban. A wannan lokacin musamman da muke yaki da cutar cikin hadin gwiwa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kan aikin kiwon lafiya, ta nuna aniyar bangarorin biyu wajen karfafa dunkulewar Sin da Afirka baki daya.

A lokacin da kasar Sin take dukufa wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kasashe da al'ummomin nahiyar Afirka sun nuna goyon baya ga kasar Sin, wanda al'ummomin kasar Sin ba za su manta ba. Kuma cikin 'yan kwanakin nan, bi da bi, kayayyakin jinya da gwamnatin kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka sun isa kasashen Afirka.

Ban da taimakon kayayyakin jinya, haka kuma, likitoci da jami'an kasashen Afirka da suka hada da Kenya, Morocco, Masar, Angola da kuma Madagascar da dai sauransu sun koyo fasahohin kasar Sin ta kafar bidiyo.

Haka kuma, sau da dama, jami'ai da masanan kasashen Afirka sun jaddada cewa, fasahohin kasar Sin suna da muhimmanci, za su kasance abin koyi ga kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

A halin yanzu, tawagogin masu aikin likitanci da kasar Sin ta tura zuwa kasashen Afirka dake kunshe da masu aikin likitanci kimanin dubu daya, suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin ba da taimako ga hukumomin kiwon lafiyar kasashen da abin ya shafa, wajen karfafa ayyukansu na yin kandagarki, da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China