Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yakar COVID-19 na bukatar hadin gwiwa maimakon rarrabuwar kawuna
2020-04-25 15:45:03        cri

A kwanakin nan yanayin da 'yan kasashen Afirka suke ciki a birnin Guangzhou na kasar Sin na jan hankalin jama'a. Sai dai wasu kafofin watsa labaru na kokarin zuzuta halin da ake ciki, inda abubuwan da suka bayyana suka sabawa ainihin abin da ya faru.

Yanzu a nan kasar Sin an samu shawo kan yanayin bazuwar cutar COVID-19 a cikin gida, sai dai ana ci gaba da samun mutanen da suka shigo kasar daga kasashen waje, wadanda ke dauke da kwayoyoin cutar COVID-19. Sa'an nan birnin Guangzhou wata cibiyar kasuwanci ce ta kasar, inda ake samun baki 'yan kasashen waje dake kai da komo, lamarin da ya sa birnin ke fuskantar hadarin samun yaduwar cutar COVID-19 matuka.

A kwanakin baya an yi gwaje-gwajen kwayar cutar COVID-19 kan 'yan kasashen Afirka 4553 dake zama a birnin Guangzhou, daga baya an gano cewa wasu 111 daga cikinsu na dauke da kwayar cutar. Batun nan ya nuna cewa 'yan Afirka da suke zama a birnin Guangzhou na fuskantar hadarin yaduwar cutar cikin al'ummarsu.

Don tabbatar da lafiyar mutanen Sin da na kasashen waje dake zaune a birnin Guangzhou, hukumar birnin ta fara tsaurara matakan dakile yaduwar cuta a ranar 4 ga watan Afrilu, inda aka yi gwaje-gwajen kwayar cuta kan dukkan mutanen da suke fuskantar yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19, gami da killace dukkan mutanen da suka shiga birnin daga kasashen ketare, inda aka sanya su zama cikin dakuna har tsawon kwanaki 14. Yayin da ake daukar wadannan matakai a birnin Guangzhou, an killace mutane dubu 15, cikin su har da 'yan kasashen waje fiye da 4600, wadanda suka zo daga kasashen Afirka, gami da Amurka, da Australia, da Rasha, da dai sauransu. Hakan na nufin an dauki matakan ne don dakile yaduwar cuta kawai, ba wai domin "kyamar 'yan Afirka" ba.

Sai dai yayin da ake gudanar da matakan na kandagarkin cutar COVID-19 a Guangzhou, an samu wasu 'yan kasashen Afirka da suka gamu da matsala sakamakon rashin fahimta da aka samu tsakanin wasu bangarori. Dagane da batun, gwamnatin kasar Sin ta bada cikakken muhimmanci, gami da daukar matakai don ba su kulawa. Yanzu ana kula da lafiyarsu ba tare da nuna bambanci tsakaninsu da mutanen kasar Sin ba, haka zalika an kebe wasu otel domin 'yan kasashen waje dake bukatar killacewa ta kwanaki 14 su zauna a ciki. Idan ba zu iya biyan kudin otel ba, to, sai a yafe musu kudin. Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Sin tana musayar ra'ayi da kasashen Afirka a kai a kai, don neman daidaita batun nan ba tare da haddasa rashin fahimta, ko kuma lalata huldar dake tsakanin Sin da Afirka ba. Ma iya cewa, bisa kokarin da bangarorin Sin da Afirka suka yi, an riga an samu daidaita wannan batu, duk da cewa har yanzu akwai wasu hotunan bidiyon da ake watsawa ta shafin sada zumunta. Hakika bai kamata a ci gaba da fushi sabo da wani abun da ya riga ya wuce ba. Kar mu manta, an dauki tsauraran matakan kandagarki a kasar Sin ne don hana yaduwar cutar COVID-19, da kare lafiyar jama'a. Wasu daga cikin 'yan Afirka dake zaune a Guangzhou sun gamu da matsala cikin dan lokaci, amma yanzu suna da wurin zama, da abinci. Sa'an nan ana kokarin kula da lafiyarsu, ba za su rasa rayuka sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 ba. Hakika a wannan lokaci na musamman, kasashen Afirka da kasar Sin suna bukatar kara hadin gwiwa don tinkarar annobar COVID-19 tare, maimakon rarrabuwar kawunan. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China