Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Don me wasu 'yan siyasar Amurka suke dinga yada jita-jitar bullowar kwayar cutar COVID-19 daga dakin gwaji?
2020-04-24 20:41:08        cri

A 'yan kwanakin baya, wasu 'yan siyasar kasar Amurka, ciki har da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, sun rika cewa wai kwayar cutar COVID-19, ta fito ne daga dakin gwaji dake birnin Wuhan na kasar Sin, sakamakon haka, wasu masu sauraronmu, da masu karanta shafinmu dake Facebook, sun fara yarda da wannan ra'ayi nasu. Amma kawo yanzu, masu nazarin ilmin kimiyya, wadanda suka fito daga Jamus, da Australiya, da Birtaniya, da Belgium, da Faransa, kamar Farfesa Edward Holmes, wanda ke nazarin ilmin kwayoyin cuta a jami'ar Sydney, da Mr. Nigel McMillan, direktan sashen nazarin cututtukan annoba, a cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Menzies dake jami'ar Griffith ta Queensland na kasar Australiya, dukkansu sun tabbatar da cewa, har yanzu ba a samu shaidar dake tabbatar da zaton cewa, "kwayar cutar COVID-19 ta bullo daga dakin gwaji" ba.

To amma ko mene ne ya sa wasu 'yan siyasar Amurka suke tabbatar da cewa kwayar cutar ta bullo daga dakin gwaji na Wuhan? A gani na, akwai dalilai hudu dake sanya su bayyana hakan.

Da farko dai, 'yan siyasar Amurka, musamman shugaba Donald Trump, da mabiyansa, suna son mayar da alhakin da ya kamata su dauka a wuyan kasar Sin, ta yadda za su iya rufe kuskuren da suka yi a farkon lokacin barkewar kwayar cutar a kasar Amurka, wato a lokacin da cutar ta bullo a kasarsu, ba su mai da hankali kamar yadda ya kamata ba, har ma Donald Trump ya ce, wannan ba sabuwar kwayar cutar Korona ba, kawai kwayar cutar numfushi ce ta yau da kullum. Sun bata dogon lokacin da ya kai tsawon watanni 2 ko fiye.

Bayan annobar ta barke a birnin Wuhan na kasar Sin, tun daga farkon watan Janairun bana, ko da yake ba a san wace irin cutar numfashi ba ce, amma ba tare da bata wani lokaci ba, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta sanar wa ofishin hokumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO dake kasar Sin dukkan bayanai game da wannan cutar numfashi. Haka nan ita hukumar WHO ma ta sanar wa kasashe mambobinta nan da nan.

Bugu da kari, ko da yake a tsakanin kasar Sin da Amurka, babu yarjejeniyar game da yadda za su yi hadin gwiwa idan wata matsalar kiwon lafiya ta faru ba zato, amma shugaban hukumar rigakafi da yakar cututtuka ta kasar Sin, ya sanar wa takwaransa na kasar Amurka wannan annobar da ta faru a kasar Sin ta wayar tarho a farkon shekarar bana.

Dalili na biyu da ya sa wasu 'yan siyasar kasar Amurka suka dinga zargi kasar Sin shi ne, tabbatar da ganin Donald Trump ya cimma nasarar babban zaben da za a yi a watan Nuwamban bana. Yanzu, sabo da Donald Trump da gwamnatinsa ba su dauki matakan yakar cutar kamar yadda ake fata ba a kasarsu, Donald Trump da gwamnatinsa sun sha zarge-zargen daga jama'a fararen hula, da kafofin watsa labaru da wasu 'yan siyasa, kamar yadda tsohon shugaba Barack Obama ya yi.

Sabo da haka, Donald Trump da gwamnatinsa sun dauki matakin mayar da idon jama'a kan kasar Sin, ta yadda za su iya rage illolin da ake yi wa Donald Trump wanda ke kokarin neman wa'adi na biyu na shugabancin kasar Amurka a karshen shekarar bana.

Dalili na uku shi ne, kasar Amurka tana son hana karin ci gaban kasar Sin bisa wannan hujja ta barkewar cutar COVID-19. Sanin kowa ne, yanzu yawan tattalin arzikin kasar Sin yana matsayi na biyu a duk duniya bayan kasar Amurka kadai. An kuma yi hasashen cewa, a shekarar 2030, yawan GDP na kasar Sin zai wuce na kasar Amurka, inda Sin din za ta hau kan matsayi na farko a fannin karfin tattalin arziki. Sakamakon hakan, a ganin wasu 'yan siyasar Amurka, kasar Sin na kawo wa kasarsu barzana, kuma dole ne ta dauki matakan hana ci gaban kasar Sin. Bayan annobar ta barke a kasar Sin ba zato, a ganinsu, wannan ya zama wata kyakkyawar damar cimma burinsu na hana bunkasar kasar Sin.

Daga karshe dai, a gani na, wani dalili na daban da ya sa wasu 'yan siyasar Amurka suka dinga yada jita-jitar shi ne, suna son illata huldar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.

Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duk duniya, kuma ta dade tana kokarin bunkasa huldar hadin gwiwa irin ta sada zumunta tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa, kuma irin wannan hadin gwiwa ya samu kyakkyawan sakamakon gani. Alal misali, a cikin dimbin shekarun da suka gabata, kasar Sin ta yi kokarin taimakawa kasashen Afirka wajen neman ci gaba, kasashen Afirka ma na taimakawa kasar Sin a fannoni da dama. Huldar sada zumunta irin ta abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ta samu amincewa daga al'ummomin bangarorin biyu. A kullum, al'ummominsu na yin mu'amala da cudanya. Idan kasar Amurka ta cimma nasarar bata wannan huldar sada zumunta irin ta abokantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka, shi ke nan, hadin gwiwar dake tsakaninsu za ta mutu, kyakkyawan sakamakon da suka samu ma zai bace kamar ya bi ruwa.

Abokan arzikinmu, ya dace mu yi hadin gwiwa wajen yakar wannan cuta, ta yadda za mu iya shawo kan ta sannu a hankali. Kamar yadda farfesa Hassan Vally, wanda ke nazarin ilmin annoba a jami'ar La Trobe ta kasar Australiya ya bayyana cewa, wasu mutane suna yada jita-jita ne a yunkurinsu na cimma wani buri nasu na siyasa, "dole ne a kula, domin kada a samar wa masu yada jita-jita wata dama." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China