Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Pompeo bai san "kyan alkawari" ba
2020-04-11 20:17:17        cri
Kasar Amurka ta sake yin alkawarin taimakawa sauran kasashe a kwanakin baya, inda sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya ce, kasarsa za ta samar da tallafin da yawansa zai kai dala miliyan 225 ga kasashe daban daban don taikamawa ayyukan dakile yaduwar cutar COVID-19 a duniya. A cewar mista Pompeo, "babu wata kasa da za ta fi kasar Amurka karamci". Sai dai tambaya ita ce, ko kasar Amurka za ta cika alkawarin da ta yi a wannan karo?

Mutanen duniya ba za su manta ba, a farkon watan Fabrairun bana, mista Pompeo ya taba sanar da cewa, kasar Amurka za ta samar da tallafin kudi dala miliyan dari 1 ga wasu kasashe, ciki har da kasar Sin. Sa'an nan zuwa karshen watan Maris, mista Pompeo ya sake bayyana cewa, kasar Amurka za ta ware kusan dala miliyan 274 don tallafawa duniya.

Sai dai daga bisani an gano cewa, dala miliyan 274 da kasar Amurka ta yi alkawarin bayarwa a karo na biyu, hakika ya kunshi dala miliyan 100 da ta ce za ta bayar a karo na farko. Ban da wannan kuma, cikin sabon tallafi karo na biyu na dala miliyan 174 da kasar Amurka ta ce za ta ba sauran kasashe, za a cire dala miliyan 64 da za a ba ofishin kwamishina mai kula da ayyuka masu alaka da 'yan gudun hijira a karkashin MDD, sa'an nan za a raba sauran miliyan 110 ga wasu kasashe 64, wadanda kowanensu ba za su samu da yawa ba.

Sai dai yanzu mun kai wata tambaya da ta fi muhimmanci, wato ko a gaskiya an samu wannan kudi? To, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya riga ya ba mu amsa a kwanakin baya, inda ya ce, "Ko kwabo daya ba mu samu ba."

Malam Bahaushe ya kan ce, "Kyan alkawari cikawa." To, kalaman da mista Pompeo ya yi, da yadda yake aikatawa, sun nuna mana cewa hakika bai san mene ne "kyan alkawari" ba.

Yadda mista Pompeo yake yi ya nuna shi da abokan aikinsa ba su lura da aikin dakile yaduwar cutar COVID-19 a duniya ba, maimakon haka suna tsoron ganin kasar Amurka ta rasa damar yin babakere a duniya. Tallafi ya shafi rayukan mutane masu rauni, duk da haka 'yan siyasan kasar Amurka sun mai da shi batun siyasa.

Sai dai a wannan lokacin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19 a kasashe daban daban, ana bukatar hadin gwiwar daukacin bil Adama, da taimakon juna a tsakaninsu, maimakon makarkashiyar siyasa da yunkurin ta da rikici. Yanzu duk mutanen duniya na jiran ganin yaushe kasar Amurka za ta cika alkawarin da ta yi, har karo da dama na samar da tallafi ga sauran kasashe. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China