Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An binne adadi mai yawa na mutanen da suka mutu sanadiyyar COVID-19 a Amurka a boye, sannan an kori wasu ma'aikatan lafiya
2020-04-11 21:10:10        cri
Ya zuwa yau, adadin sabbin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Amurka ya zarce dubu 500 kuma adadin wadanda suka mutu ya zarce 18,000, yayin da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu a jihar New York ta kasar ya zarce na kowace kasa a duniya.

A ranar 10 ga watan Afrilu, rahoton safiya na kafar CBS ya ruwaito cewa, saboda yawan wadanda suka mutu sanadiyyar cutar, ya zarce adadin da motuwarin asibiti zai iya dauka, gwamnati ta tona kabari a tsibirin Hart, makabarta mafi girma a kasar da ya shafe shekaru 150, inda aka binne gawarwakin da iyalansu ba su dauka ba.

Ban da kaduwa da wannan mataki, hankalin al'umma ya kuma koma kan matsalolin da tsarin lafiyar Amurka ke fuskanta. Ce-ce-ku-ce ya tashi daga kan matsanancin rashin kayayyakin kariya ga jami'an lafiya zuwa dalilin da ya sa aka kore su.

Kafafen yada labarai irinsu New York Times da fitaccen shafin yada labarai na website na Vox dake Amurka, sun mayar da hankali kan korar ma'aikata a asibitocin kasar.

A cewar rahotannin Vox, a watan farko da aka samu barkewar cutar COVID-19, an sallami kimanin ma'aikatan lafiya 43,000 daga aiki a fadin Amurka. Wannan ba abu ne da aka saba gani ba. Saboda bayanai sun nuna cewa, idan yanayin tattalin arziki ba shi da kyau, ba a sallamar ma'aikatan lafiya.

Yayin da ake fuskantar wannan annoba, yawan ma'aikatan lafiya da ba sa aiki ya kai wani matsayi da ba a gani ba cikin shekaru 30.

Daga bangaren New York Times da sauran kafafen yada labarai, wannan mataki ba shi da alaka da matsalar kudi daga asibitoci. A cewarsu, bisa la'akari da tsananin annobar, gomman jihohi a kasar sun ba asibitoci umarnin dakatar da tiyatar da ba ta gaggawa ba domin bada damar amfani da karin kayayyakin kiwon lafiya wajen kula da wadanda suka kamu da cutar COVID-19. Saboda haka, kudin shigar asibitoci ya ragu sosai. A don haka, aka rage adadi mai yawa na ma'aikatan lafiya ko aka kore su ko aka tilasta musu daukar hutu. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China