Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kan dukkanin sassa ne kadai mafita a yakin da duniya ke yi da COVID-19
2020-04-23 21:08:29        cri

Dukkanin mai nazartar abubuwan dake wakana a watannin baya bayan nan, ya kwana da sanin cewa ba wani batu daya tilo dake yamutsa hazo, da jan hankulan al'ummar duniya, sama da yakin da ake yi da cutar numfashi ta COVID-19, cutar da ta zame wa duniya ala-ka-kai, ta kuma kewaya kusan dukkanin nahiyoyi.

Ya zuwa ranar Alhamis 23 ga watan nan na Afrilu, alkaluma sun nuna cewa, cutar ta harbi mutane sama da 2,600,000, yayin da ta hallaka mutane sama da 180,000, kuma wasu 726,000 da 'yan kai suka warke, bayan sun yi fama da ita.

Ko shakka babu, wannan cuta ta zama gagarumar annoba da ta zama wajibi duniya ta dinke waje guda domin magance ta, duba da cewa baya ga kasancewarta kalubalen lafiya, a hannu guda kuma, ta haifar da durkushewar tattalin arzikin duniya, ana kuma hasashen za ta kai ga tsananta karancin abinci, da kara alkaluman mutane da ke cikin matsanancin hali na fatara da talauci a sassan duniya daban daban.

COVID-19 ta raba dubun dubatar al'ummu da ayyukan su, ta durkusar da masana'antu, da hada hadar kasuwanci, da harkokin sufuri, da ma sauran harkokin na jin dadin al'umma masu samar da kudaden shiga, haraji da guraben ayyukan yi. Hakan ya kuma ya sa masharhanta da dama ke ta tofa albarkacin bakin su, game da matakan da ya kamata a bi, domin tabbatar da nasarar ganin bayan cutar ba tare da wani jinkiri ba. Matakin da aka yi imanin zai taimaka wajen farfadowar al'amura, kafin kuma a dora tubalin sake ginin harkokin yau da kullum da suka riga suka durkushe.

Wani abun damuwa kuma shi ne, yadda hasashen da babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi ke nuni da cewa, wannan cuta za ta dade duniya na fama da ita, wato dai mai yiwuwa a kwashe karin watanni nan gaba, kafin a kai ga shawo kan ta baki daya. Don haka babban abun tambaya a nan shi ne, wadanne hanyoyi ne mafiya dacewa a bi, domin ganin bayan wannan cuta cikin hanzari?

Amsar wannan tambaya dai kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka sha nanatawa shi ne, dagewa wajen hadin gwiwa tsakanin sassan duniya daban daban, musamman a fannonin musayar bayanai na kwararru, game da yanayin yaduwar cutar, da hanyoyin dakilewa, da na shawo kan ta. Sa'an nan a tallafawa kasashe masu rauni da kayayyakin kariya, da magunguna da suke bukata domin a gudu tare a tsira tare.

A nan ya zama wajibi, duniya ta jinjinawa kwazon kasar Sin, da sauran kasashe masu manufa irin ta Sin, wadanda suka fahimci darajar agazawa sauran kasashe masu rauni, da ma manyan kasashen duniya da wannan annoba ta yiwa kamun kazar kuku. Musamman duba da cewa, COVID-19 ta zamewa duniya tsumagiyar kan hanya fyadi yaro fyadi babba.

Masana da dama na jaddada cewa, yanzu ba lokaci ne na zargin juna, ko siyasantar da batun wannan cuta ba. Lokaci ne na aiki tare, da taimakekeniya, da jin kan juna, duba da cewa, abun da ya ci doma ba fa zai bar awe ba!! (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China