Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labaran Amurka: Fadar White House ta samu wadanda za ta shafawa kashin kaji
2020-04-11 20:41:14        cri
Kafar yada labarai ta The Associated Press ta Amurka, ta ruwaito a ranar 9 ga wata cewa, yayin da ake fuskantar sabuwar annoba, shugaban kasar Donald Trump na shafawa wasu kashin kaji domin dauke hankalin jama'a daga kurakuren da gwamnatinsa ta tafka.

A wani yunkuri na ba fadar White House damar nisanta kanta daga yawan mutanen da suke mutuwa, Shugaba Trump ya nemi wadanda zai shafawa kashin kaji.

A lokacin da ake fuskantar wannan annoba, watanni 7 kafin kada kuri'a, wannan yunkurin na karuwa cikin sauri.

Jerin wadanda shugaba Trump ke dorawa laifi na karuwa, haka kuma suna sauyawa.

An zargi wani gwamnoni 'yan jam'iyyar Democrat da rashin yin abun da ya kamata yayin da ake fama da annobar. Da farko, an zargi kafafen yada labarai da zuzuta hadarin cutar, kuma aka zarge su da rashin yabawa matakan da gwamnati ke dauka na tunkarar cutar. Har ila yau an ce jami'an sa ido na sassan gwamnati daban daban na shirya manakisar da za ta sa a ga bakin fadar White House da rashin cikakken shiri. Da farko dai bai zargi kasar Sin ba, amma daga baya, ta zargi kasar Sin da wai laifin boye bayanan lafiya mai muhimmanci. Yanzu kuma hukumar lafiya ta duniya aka dorawa laifi, inda Trump ya yi barazanar daina samar mata kudi. A takaice dai, Shi dai Trump ba shi da wani laifi ko kadan.

A watan da ya gabata, lokacin da kasar ta fara aiwatar da matakan killace kai, Trump ya bayyana cewa shi babu wani hakki dake kansa dangane da batun rashin isassun kayayyakin gwaji. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China