Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Zimbabwe sun taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya
2020-04-18 17:12:46        cri
A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, sun taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu, inda suka yi alkawarin kara karfafa hadin gwiwar kasashensu.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin da Zimbabwe sun kiyaye aminci a tsakaninsu tare da marawa juna baya, yana mai cewa dangantakarsu dadaddiya ce da ta jure sauye-sauyen yanayin duniya.

Da yake bayyana cewa shi da takwaran nasa na Zimbabwe sun cimma matsaya kan muhimman batutuwan da suka shafi raya dangantakar dake tsakanin kasashensu, shugaba Xi ya ce, yana ba dangantakarsu muhimmanci gaya, kuma a shirye yake ya hada hannu da shi wajen amfani da cikar dangantakarsu shekaru 40, a matsayin wata dama ta kara samun nasarori.

Ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, a shirye Sin take ta bunkasa hadin gwiwarta da Zimbabwe wajen shawo kan kalubalen COVID-19 da duniya ke fuskanta.

A nasa bangaren, shugaba Emmerson Mnangagwa, ya ce shekaru 40 da suka gabata, sun nuna cewa, rikon gaskiya da aminci da goyon baya da moriyar juna, su ne muhimman abubuwan dake kyautata alakar 'yan uwantaka tsakanin kasashen biyu.

Ya ce Zimbabwe na kan bakanta na kiyaye manufar kasar Sin daya tak a duniya da kuma hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, yana mai cewa kasarsa zata ci gaba da karfafa dangantakar kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China