Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta karfafa bincike kan muhimman fasahohi na zamani
2020-04-20 09:56:00        cri
Mataimakin ministan masana'antu da fasahohin zamani na kasar Sin (MIIT) Chen Zhaoxiong, ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara zage damtse wajen karfafa yin binciken fasahar kere-kere don gina da ma amfani da muhimman fasahohi na zamani.

Ministan ya ce, ya kamata a kara ba da taimako, don gudanar da bincike da inganta fasahar 5G da 6G, a yayin da ake daidaita harkokin kirkire-kirkire, ya dace a bunkasa masana'antu da sassan zuba jari da manufofi.

Bugu da kari, Chen ya jaddada muhimmancin karfafa bukatar farfado da fasahar zamani da inganta sabuwar fasahar zamani don saukaka harkokin kasuwanci da inganta rayuwar al'ummar kasar.

Ya ce, ma'aikatarsa za ta dauki managartan matakai da suka dace, don bunkasa masa'antu, kamar hanzarta gina fasahar 5G da tsarin Intanet da zai hade jama'a, na'urori da sauran abubuwa, yayin da ake kokarin daga darajar kananan cibiyoyin tattara bayanai, karfafa cin gajiyar manhajoji da gina tsarin intanet mai cike da tsaro.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China