Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yanayin karatu a Jihar Xinjiang ta kasar Sin ya inganta
2020-04-20 10:07:33        cri
Wani Malami dan kasar Jamus, Micheal Heinrich, ya gano cewa, ana tabbatar da 'yancin samun ilimi ga al'ummar Uygur da sauran kabilun dake jihar Xinjiang ta kasar Sin yadda ya kamata, inda ya ce matasa a yankin na more karin damarmaki masu kyau.

Micheal Heinrich, wanda ya kasance malami a Jami'ar Minzu ta kasar Sin cikin sama da shekaru 5, ya bayyana cikin wata mukala da aka wallafa a shafin website na kafar yada labarai ta Khabar a cikin watan Maris cewa, a shekarun baya-bayan nan, dalibai musulmi na iya inganta basirarsu da yin aiki tukuru da kansu da kyautata yanayin zaman rayuwarsu, ta hanyar ilimin sana'o'in hannu.

A cewar mukalar, Jihar Xinjiang ta fuskanci matsalolin da suka hada da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da fafutukar neman ballewa, don haka bada ilimin sana'o'in hannu da horo a yankin, ingantaccen mataki ne na karfafa doka da kare muhimman muradun dukkan kabilun dake yankin.

Haka zalika, yunkuri ne na yaki da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci da nufin samar da kwanciyar hankali a jihar.

Micheal Heinrich ya kara da cewa, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma da ma 'yan siyasar Amurka, na sokar gwamantin kasar Sin ta hanyar fakewa da 'yancin bil adama, wanda ba watsi kadai ya yi da gaskiyar lamarin ba, har ma da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin.

Da yake bada misali da wasu da suka ziyarci Jihar Xinjiang, ya ce yanayin da suka gani, ya banbanta sosai da labaran da wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaran kasashen yamma ke yadawa.

Ya ce ana kare 'yancin rayuwa da samun ci gaba na dukkan kabilun yankin yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China