Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira taron namena labarai kan yadda aka gyara yawan mazauna birnin Wuhan da suka mutu sakamakon cutar COVID-19
2020-04-17 15:01:02        cri

Yau ranar 17 ga wata, ofishin dake jagorantar ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar COVID-19 na birnin Wuhan da ke kasar Sin, ya ba da wata sanarwa kan yadda ake gyara yawan mazauna birnin Wuhan da suka kamu da cutar da ma wadanda suka mutu sakamakon cutar. A wannan ranar kuma, an kira taron manema labarai, inda mai kula da wannan aiki na ofishin ya amsa tambayoyin manem labara.

1. Me ya sa ake gyara yawan mazauna birnin Wuhan da suka kamu da cutar COVID-19 da ma wadanda suka mutu sakamakon cutar.

Annobar COVID-19 wani lamarin lafiyar jama'a ne na ba zata da ke samun matukar saurin yaduwa, da shafar mafiya yawan mutane, da ma matukar wuyar dakilewa, tun bayan kafuwar kasar Sin a shekarar 1949. Birnin Wuhan ma wuri ne da cutar ta fi kamari, wanda kuma ya kasance muhimman jigo a wajen samun nasara a kan cutar.

Bayan da aka dauki tsauraran matakan dakile yaduwar cutar daga dukkan fannoni, yanzu an riga an shawo kan cutar, har ma an sake bude hanyoyin shige da fice na birnin. Lamarin da ya samar da sharadi mai kyau ga gudanar da ayyukan gyaggyara kididdigar da ta shafi annobar.

Sabo da gaza karbar masu kamuwa da cutar a farkon bullar cutar a Wuhan, da gudanar da ayyukan jinya fiye da kima don ceton mutane, da ma gaza shiga tsare-tsaren tattara bayanai na intanet a kan lokaci da wasu hukumomin jinya suka yi, ba a iya sanar da bayanan masu dauke da cutar da wadanda suka mutu a kan lokaci ba. Don haka, bisa "Dokar kandagarki da shawo kan cuttuttuka masu yaduwa ta Sin", da "Ka'idojin tinkarar lamuran kiwon lafiyar jama'ar ba zata", da "Ka'idojin gudanar da ayyukan kididdiga na Sin", da "Ka'idojin tafiyar da harkokin yin rajista kan bayanan matattu na kasar", ya kamata a gyara yawan mazauna birnin Wuhan da suka kamu da cutar, da ma wadanda suka mutu sakamakon cutar.

2. Ta yaya aka gudanar da aikin gyara adadin?

Ofishin dake jagorantar ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar COVID-19 na birnin Wuhan mai dora matukar muhimmanci kan wannan aiki, kuma bisa aniyar mutunta tarihi, da al'umma, da ma matattu, an yi gyare-gyaren bisa hakikanin abun. A karshen watan Maris, an kafa kungiyar bincike kan alkaluman da suka shafi annobar, da ilmin cututtuka masu yaduwa, wadda bisa hadin kai tare da hukumomin da suka shafi kiwon lafiya, yaki da cututtuka, tsaron jama'a, harkokin jama'a, shari'a, kididdiga na birnin. Sa'an nan an sake tattara bayanan dukkan wadanda suka kamu da cutar daga tsare-tsaren intanet na tattara bayanan yadda aka dakile yaduwar cutar, bayanan matattu, bayanan masu kamuwa da cutar a asibitoci, da bayanan sakamakon binciken lafiyar mutane na birnin, baya ga sake tattara bayanan daga wuraren da suka shafi annobar, kamar sassan kula da masu zazzabi, asibitocin yau da kullum, asibitocin wucin gadi, wuraren killacewa, unguwanni masu ganon wadanda ke kamuwa da cutar, da gidajen kurkuku, da hukumomin kula da tsoffi na gwamnati. Daga baya kuma an sake yin kididdiga bisa taimakon hukumomin jinya, unguwanni, ofisoshin 'yan sanda, wuraren aikin wadannan mutane da ma iyalansu.

3. Akwai sauyin alkaluma bayan da aka sake yin kididdiga kan mazauna birnin da suka kamu da cutar COVID-19, da wadanda suka mutu sakamakon cutar?

Ya zuwa karfe 12 na daren ranar 8 ga watan Afrilu, yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu da 325 a birnin bayan da aka sake yin kididdiga, lamarin da ya sa yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai 50,333 gaba daya. Yayin da yawan mazauna birnin da suka mutu sakamakon cutar ya karu da 1290 bisa adadin da aka bayar a baya, hakan ya sa aka gyara yawan matattu sakamakon cutar har zuwa 3,869 a birnin.

4. Wace irin ma'ana wannan aikin gyare-gyaren zai bayar?

Lafiyar jiki babban buri ne na jama'a. Alkaluman da ke da nasaba da annobar ba kaiwa ya shafi lafiyar jikin mutane ba ne, har ma yana da nasaba da amincewar da ake nuna wa gwamnati. Aikin gyara alkaluman da suka shafi wadanda suka kamu da cutar, da wadanda suka mutu sakamakon cutar, ba ma kawai zai taimaka wajen kiyaye muradun jama'a ba ne, har ma zai taimaka wajen tsara manufofin kandagarki da dakile cutar bisa ilmin kimiyya, da fayyace abubuwan da al'umma ke mai da hankali a kai, da ma girmama ko wane rai.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China