Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Za a kara bunkasa bangaren aikin gona kasar Sin cikin shekaru 10 masu zuwa
2020-04-21 10:36:26        cri

Wani rahoto da taron dake nazarin bangaren aikin gona na kasar Sin(2020-2029) na shekarar 2020 ya fitar a jiya Litinin, ya bayyana cewa, yadda ake farfado da daga matsayin sashen aikin gonan kasar, zai yi matukar bunkasa cikin shekaru goma masu zuwa, kana za a ci gaba da inganta yadda ake zamanantar da bangaren aikin gonan kasar.

Rahoton ya yi kuma bita da nazarin yanayin kasuwar manyan kayayyakin amfanin gona guda 18 a shekarar 2019, daga bisani ya yi hasashe kan yadda za a samar da kayayyaki, da amfani da su, da cinikayya da farashin kaya a cikin shekaru goma masu zuwa, ya kuma yi sharhi kan wasu abubuwa na rashin tabbas da ka iya kunno kai.

Har ila, rahoton ya ce,mayar da hankali wajen raya sashen aikin gona na kasar, zai kartata daga samar da kayayyaki zuwa kara ingancin kayayyakin. Za kuma a ci gaba da inganta tsarin samar da kaya da raba shi ba tare da gurbata muhalli ba, cikin inganci da tsaro .

Bugu da kari, sashen aikin gona na kasar Sin, zai kara bude kofarsa ga ketare. Cinikayyar kayayyakin amfani gona na kasa da kasa zai kara bunkasa, kana kasar Sin za ta ci gaba da zama kasar dake kan gaba a fannin shigo da kayayyakin amfanin gona.

Rahoton ya kara da cewa, za a bunkasa hadin gwiwar cinikayayyar Sin da Amurka da Brazil da kasashen kungiyar ASEA da kungiyar tarayyar Turai(EU), da Australiya da kasashe dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. A hannu guda kuma, kasar Sin za ta ci gaba da shigo da kayayyakin amfanin gona daga ketare tare da kara fadada wuraren da ake shigo da irin wadannan kayayyaki. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China