Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Afirka ta Kudu tana shirin kara zuba jari da kasashen yammacin Afirka
2020-01-29 16:25:25        cri
Mataimakiyar ministan sashen cinikayya da masana'antu na kasar Afirka ta Kudu Nomalungelo Gina, ta bayyana cewa, kasarta tana shirin kara bunkasa alakar cinikayya da zuba jari da kasashen yammacin Afirka kamar Ghana da Najeriya.

Da take karin haske kan haka, minista Gina ta ce, a mako mai zuwa ne, jami'ai daga sashen cinikayya da masana'antun kasar gami da wasu 'yan kasuwa a fannonin aikin gona, da kayayyakin more rayuwa, hakar ma'adinai da magunguna su 40, za su yi kokarin kulla yarjeniyoyi a kasashen biyu.

Ziyarar za ta samarwa kamfanonin Afirka ta Kudun wani dandalin cin gajiya a fannonin cinikayya da zuba jari a kasashen Ghana da Najeriya. Bugu da kari, ziyarar wani bangare ne na karfafa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar, yayin da kasashen nahiyar ta Afirka da dama suka sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya marar shinge ta nahiyar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China