Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci a samar da zaman lafiya a yankin Great Lakes
2020-04-23 10:48:15        cri

Wakilin kasar Sin ya bukaci a kara kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Great Lakes, domin dorawa kan irin nasarorin da aka cimma a shiyyar.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce kasar tana farin ciki da irin nasarorin da aka samu a yankin na Great Lakes, kana ta yabawa kokarin da kasashen shiyyar ke yi da shugabanninsu don wanzar da zaman lafiyar yankin.

A taron kwamitin sulhun MDDr da aka gudanar ta kafar bidiyo, Zhang Jun ya ce kasar Sin tana bada kwarin gwiwa ga kasashen dake shiyyar da su kara yin hadin gwiwa domin gina tsarin siyasar amincewa da juna don kara samun ci gaba.

Ya ce ya kamata kasa da kasa su kara daukar matakan gina ci gaban shiyyar da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a dauki dukkan matakan da suka dace da suka kunshi matakan soji da wadanda ba na soji ba domin kawar da duk wata barazana da kungiyoyin masu dauke da makamai ke haifarwa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China