Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren MDD ya yi kira da a tsagaita bude wuta a duniya don tinkarar cutar COVID-19
2020-03-24 11:46:12        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita bude wuta a dukkan sassan duniya don tinkarar cutar COVID-19.

Guterres ya bayyana a gun taron manema labaru ta yanar gizo da aka gudanar a wannan rana cewa, a halin yanzu ya kamata a maida hankali kan kokarin yaki da cutar COVID-19 maimakon rikice-rikice. Ya kalubalanci bangarori daban daban da ke rikici da juna, da su rage kiyayya da fito na fito da juna, sannan su tsagaita bude wuta. A ganinsa, tsagaita bude wuta zai taimaka wajen kafa hanyoyin bada jinya, da samar da yanayin daidaita matsaloli ta hanyar diplomasiyya, da kuma sa kaimi ga tinkarar cutar COVID-19 a yankuna marasa karfin yaki da cutar.

Haka kuma, ya kalubalanci kasa da kasa da su kara hada gwiwa don tinkarar cutar. Ya ce, kamata ya yi kasashe masu arziki su taimakawa kasashe masu tasowa. Kana yana fatan za a gabatar da wasu shirye-shirye don tinkarar illar da cutar ta yi wa kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China