2020-03-23 09:42:05 cri |
A sakonsa domin ranar ruwa ta duniya, da ta fado a jiya, 22 ga wata, Sakatare Janar din ya ce albarkatun ruwa na fuskantar hadarin da ba a taba gani ba.
Antonio Guteress ya bayyana cewa, dumamar duniya da rashin amfani da ruwan ta hanyoyi masu dorewa, za su haifar da gwagwarmayar neman albarkatun ruwa da ba a taba gani ba, wanda zai kai ga raba mutane da muhallansu. A cewarsa, wannan lamari zai yi mummunan tasiri kan kiwon lafiya da samar da kayayyaki, sannan zai kara barazanar rashin kwanciyar hankali da rikici.
Da yake tsokaci dangane da mafita, Guterres ya ce dole ne a gaggauta zuba jari wajen samar da hanyoyin ruwa da tsarukan samar da ruwa, da kuma samun ingantaccen ci gaba a fannin amfani da ruwa. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China