Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashe su gaggauta dakile tasirin COVID-19 ga kananan yara
2020-04-17 11:08:30        cri
A ranar Alhamis MDD ta bukaci al'ummar kasa da kasa su gaggauta daukar matakan rage mummunan tasirin da annobar COVID-19 za ta yi wa kananan yara a fadin duniya.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a wani taron hukumar ta kafar bidiyo cewa, wannan matsala ce da tasirinta ya shafi dukkan yara, a dukkan matakan shekaru, kuma ya shafi dukkan kasashe.

Ya ce wannan gagarumar matsala ta shafi kananan yara kusan miliyan 369 a kasashen duniya 143 wadanda yawancinsu sun dogara ne kan abincin da makarantu ke samarwa, a matsayin hanyar samun abinci domin rayuwar yau da kullum, wanda kuma yake samar musu da abinci mai gina jiki. Yanzu dole ne a nemi wata hanyar da za'a cike wannan gibin.

Ya ce karin dubban daruruwan yara za su iya mutuwa a wannan shekarar, idan an kwatanta da lokaci gabanin barkewar annobar, sakamakon matsin tattalin arzikin da duniya ke fuskanta. Wannan al'amarin zai mayar da hannun agogo baya game da cigaban da aka samu a shekaru uku da suka gabata na shirin rage mace macen kananan yara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China