Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi gargadi game yada bayanan karya yayin da take kai kayayyakin yaki da COVID-19 Afrika
2020-04-15 10:30:54        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterrres, ya kaddamar da wani gangamin yaki da bayanan karya dangane da cutar COVID-19, yayin da hukumar ta fara tura kayayyakin tallafi nahiyar Afrika a wani bangare na kokarin duniya na yaki da annobar.

Yayin wani sako ta kafar bidiyo a jiya, Antonio Guterres ya ce duniya na fuskantar matsalar yaduwar bayanan karya dangane da annobar, inda ya ce mutane na tsoro, kuma suna son sanin abun da ya kamata su yi da kuma inda za su samu shawara.

Ya sanar da shirin yada bayanai dangane da aikin tunkarar cutar, wanda za a cika shafukan intanet da hakikan bayanan kimiyya domin magance labaran na karya.

Ya ce an tsara jirgin dakon kayayyakin tallafin na farko zai bar Addis Ababa na Habasha zuwa sauran kasashen nahiyar a jiya Talata, da nufin kara musu karfin yaki da cutar COVID-19

Kayayyakin wani bangare ne na shirin MDD na inganta raba kayayyakin tunkarar annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China