Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta tabbatar da kashe wasu shugabannin BH yayin luguden wuta da sojoji suka kai
2020-04-21 09:59:44        cri

Hedkwatar tsaro ta Nijeriya, ta ce an kashe wasu manyan shugbannin kungiyar BH yayin wasu luguden wuta da rundunar sojin saman kasar ta yi a baya-bayan nan, a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwar da hedkwatar tsaron ta fitar, ta ce an kai hare-haren ne a ranar 17 ga wata a garin Durbada dake jihar Borno, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Ta kara da cewa, yayin harin, an kuma lalata wasu gine-gine dake zaman maboyar 'ya'yan kungiyar.

Sanarwar dai, ba ta bayyana ainihin adadin shugabannin BH da aka kashe yayin luguden wutan ba, sai dai ta ce jiragen yakin da aka tura don gudanar da aikin, sun kai hari daidai yankin da aka auna, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu 'yan ta'adda. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China