![]() |
|
2020-04-19 15:55:24 cri |
A sakonsa na ta'aziyyar marigayin, shugaba Buhari ya ce, "Mallam Abba Kyari mutum ne mai muhimmanci a gare mu. Yana daga cikin manyan ginshikan da suka bunkasa ci gaban Najeriya".
Kyari, mai shekaru 67, wanda ya sha fama da jinya, cikakken 'dan kishin Najeriya ne, in ji shugaban kasar.
Marigayin yana daya daga cikin makusantan shugaba Buhari.
Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa, ya shafe kimanin shekaru 42 yana abota da marigayin, wanda daga bisani ya nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin kasar.
Mutuwar Kyari ta kasance a matsayin mutuwar farko na wani babban jami'in gwamnatin kasar ta yammacin Afrika tun bayan bullar annobar ta COVID-19 a kasar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China