Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya tana nuna cikakken goyon baya ga hukumar WHO
2020-04-20 12:42:21        cri

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya bayyana a baya-bayan nan a birnin Abuja fadar mulkin kasar cewa, babban daraktan hukumar lafiyar duniya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, kuma ya dauki matakai masu inganci, don haka Najeriya na nuna goyon baya ga kokarin da hukumar WHO take yi karkashin jagorancinsa na yakar COVID-19 a duniya.

Ban da wannan kuma, Geoffrey Onyeama ya shedawa manema labarai cewa, Tedros Adhanom Ghebreyesus na da cikakkiyar kwarewar jagorantar WHO, musammam la'akari da yadda yake gudanar da aikinsa da kyau wajen yakar cutar. Ya ce babban daraktan ba ya daukar matakai yadda ya ga dama, a maimakon haka, ya kan dauke su bisa bayanai da alkaluman da aka gabatar masa kan cutar, tare da yin la'akari da shawarwarin masana daban-daban. Saboda haka, a cewar minista Onyeama, Najeriya ta nuna cikakken goyon baya gare shi, da fatan ganin hukumar WHO ta ci gaba da zama karkashin jagorancinsa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China