Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram da dama yayin wani fafatawa
2020-04-20 09:37:29        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da ISWAP masu tarin yawa, yayin wani bata kashi da suka yi ranar Asabar din karshen mako a kauyen Buni Gari dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da kamfanin dillacin labarai na Xinhua na kasar Sin ya samu kwafenta a Abuja, fadar mulkin Najeriya, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar John Enechen, ya bayyana cewa, babu wani soja da ya rasa ransa ko makamansu yayin bata kashin.

A wani labarain kuma, kakakin ya kara da cewa, a wannan rana dakarun kasar sun yi nasarar kama wasu 'yan bindigar dake addabar mazauna wasu kauyuka a jihar Katsina dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Jami'in ya ce, dakarun sun dakile wani hari da 'yan bindigar suka shirya kaiwa mazauna kauyukan Kurechi da Qurzan Maikuka a karamar hukumar Dutsin-Ma dake jihar Katsina, inda suka kama wasu daga 'yan bindigar yayin wasu suka tsere da raunuka a jikinsu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China