Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya sun samar da dala miliyan 66 don yaki da COVID-19
2020-04-19 15:54:25        cri
A Najeriya kungiyoyi masu zaman kansu sun tattara kudi kimanin dala miliyan 66.7 don yaki da annobar COVID-19 a kasar, kakakin babban bankin Najeriyar ya sanar da hakan.

Cikin sanarwar da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua da yammacin ranar Juma'a, Isaac Okorafor, shugaban sashen sadarwa na babban bankin Najeriya (CBN) ya ce, wannan shi ne alkaluma na baya bayan nan na gudunmowar da ake tarawa.

A karkashin shirin na hadin gwiwa don yaki da COVID-19, Okorafor ya ce, daidaikun 'yan Najeriya da kungiyoyi masu zaman kansu, da suka hada da bankuna, suna ci gaba da bayar da gudunmawa domin tallafawa fannin kiwon lafiya da samar da muhimman kayayykin kiwon lafiya don dakile annobar COVID-19 a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China