![]() |
|
2020-04-20 14:07:18 cri |
Mai magana da yawun asusu mai taimakawa mutanen da suke fama da bala'u na VSF Munachi Okoro ya ba da wata sanarwa kwanan baya a Abuja cewa, VSF yana shirin baiwa wadanda suke cikin mawuyacin hali taimakon abinci da magunguna saboda ganin yanayin yaduwar cutar COVID-19 na tsananta a kasar. An ce wasu magidanta fiye da 27000 daga Abuja, jihar Lagos da kuma Ougun da Borno sannan da Yobe da Taraba da dai sauransu, ko wane su na iya samun shimkafa kilo 10 da wake da kuma masara, da man dafa abinci lita 4 da gishiri kilo 2, da kuma ruwan sha, da magunguna da kuma kayayyakin kangadarki. Ban da wannan kuma, rukuni na musamman na gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnantocin jihohi da dai sauransu sun hada kansu wajen fadakar da jama'a don su bi ka'idojin kiwon lafiya. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China