Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a tashoshin jiragen kasa don yaki da COVID-19
2020-04-20 10:30:30        cri
Hukumomi a Najeriya sun sanar cewa an fara aikin feshin sinadarin kashe kwayoyin cuta a dukkan tashoshin jiragen kasa dake kasar a matsayin matakan dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

Aikin, wanda aka fara tun a ranar Asabar da ta gabata, zai shafi fesa sinadaran a cikin dukkan taragan jirgin kasan da sauran dukkan kayayyaki dake tashoshin jiragen kasan na Najeriya, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen kasan Najeriyar (NRC) ta bayyana cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, wannan yana daga cikin matakan gaggawa da aka dauka domin rage hadarin yaduwar annobar COVID-19, musamman a jahar Legas, wacce ta zama wajen da cutar ta fi kamari a Najeriyar.

Za a gudanar da aikin ne daga Legas zuwa Abuja, babban birnin kasar, sai kuma dukkan ragowar bangarorin kasar, a cewar sanarwar.

A ranar 23 ga watan Maris ne aka dakatar da dukkan zirga zirgar jiragen kasa a duk fadin Najeriya, a matsayin bangare na matakan dakile bazuwar annobar COVID-19 a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China