Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ce ya kamata kungiyar G20 ta jagoranci raya huldar kasa da kasa
2019-11-23 16:48:11        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce ya kamata kungiyar G20 ta jagoranci aikin raya hulda tsakanin kasa da kasa.

Da yake jawabi yayin taron ministocin harkokin wajen kungiyar G20, Wang Yi ya ce, karfin tattalin arzikin duniya na raguwa, baya ga karuwar haddura da yake fuskanta, sannan duniyar na cike da rashin tabbas da karuwar zartar da ra'ayin kashin kai da kuma kariyar cinikayya.

Ya ce bai kamata a nade hannu ana kallo ba, yana mai cewa, hulda tsakanin kasashe daban-daban na da muhimmanci wajen warware batutuwa da dama da ake fuskanta a duniya.

Ya ce a matsayinta na babban dandalin hadin gwiwar tattalin arziki, ya kamata kungiyar G20, ta jagoranci batun raya hulda tsakanin kasa da kasa da samar da mafita domin samun ci gaban tattalin arzikin duniya mai inganci.

Ya kara da cewa, huldar kasa da kasa na gudana ne bisa dokoki da ka'idojin kasa da kasa, kuma manufar ita ce, tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba na bai daya a duniya da kuma kiyayewa da tabbatar da adalci da inganta samun moriyar juna.

Baya ga wannan, Wang Yi ya tabu batun muradun ci gaba masu dorewa, yana mai bayyanasu a matsayin hanyar magance manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.

Ya ce kawar da talauci ya zuwa shekarar 2030 na kan gaba cikin muradun, inda ya ce cikin shekaru 40 da suka shude, kasar Sin ta fitar da mutane miliyan 850 daga kangin talauci, adadin da ya dauki sama da kaso 70 na aikin yaki da talauci a duniya, yana mai cewa, kasar za ta yi ban kwana da talauci ya zuwa shekarar 2020.

Bugu da kari, ministan ya ce a shirye Sin take ta yayata gogewarta ga sauran kasashen domin taimaka musu inganta aiki fatattakar talauci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China