Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka ta Kudu na fatan taron G20 zai tabbatar da goyon-baya ga kasashen dake tasowa
2019-06-27 12:13:58        cri
Mai magana da yawun shugaban kasar Afirka ta Kudu Khusela Diko ya bayyana jiya Laraba cewa, kasarsa za ta yi amfani da taron kolin kungiyar kasashen G20 wanda za'a bude gobe Jumma'a a birnin Osakar kasar Japan, don tabbatar da samun goyon-baya ga kasashen Afirka da sauran wasu kasashen dake tasowa wajen cimma burin samun dauwamammen ci gaba.

Kakakin ya bayyana cewa, ya kamata a maida hankali kan yaki da hada-hadar kudi ta haramtacciyar hanya dake hana kasashen Afirka amfani da albarkatun kasa da ya kamata a ce an yi amfani da su wajen samun ci gaba.

Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya shiga cikin harkokin kasa da kasa tun bayan da aka rantsar da shi a watan Mayun bana.

Taron kolin G20 a bana zai maida hankali kan wasu muhimmman fannoni takwas, ciki har da raya tattalin arzikin duniya, da kasuwanci da zuba jari, da kirkire-kirkire, da kiyaye muhallin halittu da raya makamashi, da samar da guraban ayyukan yi, da karfafa gwiwar mata, da neman ci gaba da kuma kiwon lafiya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China