Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin G20 sun yi alkawarin samar da muhallin zuba jari da cinikayya cikin 'yanci da adalci
2019-06-29 16:43:18        cri

An kammala taron kungiyar G20 a yau Asabar, da alkawarin ci gaba da bude kofa da samar da muhallin cinikayya da zuba jari cikin adalci da 'yanci ba tare da wariya ba.

Yarjejeniyar da shugabannin G20 suka cimma yayin taron, ta ce cinikayya da zuba jari muhimman abubuwa ne dake raya ci gaba da bunkasa ayyukan samar da kayayyaki da hidimomi da kirkire-kirkie da samar da ayyukan yi da kuma ci gaba.

Da suke jadadda goyon bayansu ga yi wa hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) garambawul, domin inganta ayyukanta, shugabannin na kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, sun ce za su yi aiki da sauran mambobin hukumar, domin share fagen taro na 12 na ministocin kasashe mambobinta.

Sun kuma amince su dauki matakan da suka dace game da aikin tsarin warware takaddama na hukumar, bisa ka'idojin da mambobinta suka daddale. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China