Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta taimakawa Afrika ta cimma burinta nan ba da dadewa ba
2019-11-23 20:31:19        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, ya ce a shirye kasar take ta yi dukkan mai yiwuwa wajen taimakawa nahiyar Afrika cimma burinta nan ba da dadewa ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da yake halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a Nagoya na Japan.

A cewarsa, domin taimakawa nahiyar cimma muradun ci gaba masu dorewa, akwai bukatar a mayar da hankali wajen magance manyan matsaloli 3 da suka hada da rashin kayayyakin more rayuwa da rashin basira da karancin kudi, tare kuma da magance matsalolin rayuwar yau da kullum da suka hada da aikin yi da wadatar abinci da tufafi da kiwon lafiya.

A don haka ya ce, kasar Sin za ta rungumi ka'idar tabbatar da adalci da gaskiya da samun sakamako da aiki tukuru domin taimakawa nahiyar Afrika samun ci gaba.

Ministan ya ce kasar Sin ta taimaka wajen gina sama da kilomita 10,000 na tituna da sama da kilomita 6,000 na layukan dogo da adadi mai yawa na dakunan karatu da makarantu da asibitoci da sauran abubuwan kyautata rayuwa a fadin nahiyar, wadanda suka taimaka wajen samun ci gaba a wuraren.

Baya ga haka, an aiwatar ko kuma an dau hanyar aiwatar da sama da rabin shirye-shirye 8 da taimakon kudi da aka sanar yayin taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC da aka yi a bara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China