Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dangantakar Sin da Afrika na inganta a cikin hadin kan da suke yi wajen yakar COVID-19
2020-04-20 11:29:42        cri

Kwanan baya, tawagar likitoci ta kasar Sin wadda ta isa kasar Burkina Faso ta fara aikinta a kasar.

Ranar 18 ga watan da muke ciki bisa agogon wurin, tawagar ta kai ziyara asibiti mafi girma na kasar, inda ake karbar wadanda suka kamu da cutar COVID-19, don yin taron karawa juna sani kan cutar tare da likitocin sassan daban-daban na asibitin, ta yadda za su raba fasahohi da dabarun kasar Sin, a fannin jinyar majiyyata masu kamuwa da cutar COVID-19, tare da likitocin kasar Burkina Faso.

Ban da ayyukan da wadannan likitocin kasar Sin suke yi, tallafin kayyayakin da gwamnatin Sin da kuma gidauniyar Ma Yun suka bayar sun isa kasashen Afrika bi da bi, matakan da suka samu yabo matuka daga kasashen.

Taimakawa kasashen Afrika wajen dakile wannan mummunar cuta, nauyi ne dake wuyan kasar Sin, a matsayinta na kasa mai karfi, kuma taimako ne da ya kamata Sin ta baiwa 'yan uwanta na nahiyar Afrika.

Danganatakar Sin da Afrika na da inganci sosai wadda ba a iya canjawa ko illatawa, kuma ba wanda zai hana bunkasuwar dangantakar bangarorin biyu ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China