Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar ECA ta bukaci a sauya tsarin tattalin arziki domin samar da ayyuka masu dorewa ga matasan Afrika
2019-12-05 11:12:15        cri

Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD(ECA), ta ce sauya tsarin tattalin arziki ita ce hanya mafi dacewa ta samar da ayyukan yi ga al'ummar Afrika dake kara yawa.

Daraktan sashen kula da harkokin tattalin arziki da shugabanci na hukumar ECA, Adam Elhiraika ne ya bayyana haka, yana mai cewa, akwai bukatar sauya tsarin tattalin arzikin nahiyar Afrika da kuma daina haka da fitar da kayayyakin da ake sarrafawa, saboda bisa yanayin da ake ciki a yanzu, ba za a taba cimma bukatar samar da guraben ayyukan yi miliyan 10 a ko wace shekara a nahiyar ba.

Wata sanarwa da hukumar ECA ta fitar, ta ruwaito Daraktan na bayyana haka ne yayin taro kan tattalin arzikin nahiyar Afrika na 2019 dake gudana, inda ya jaddada cewa, nahiyar Afrika na bukatar sabuwar dabarar da za a samar da ita a nahiyar, wadda kuma za ta iya taimakawa wajen kara darajar kayayyakin nahiyar tare da ba su damar yin gogayya a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China