Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yabawa taimakon da Sin ke baiwa fannin kiwon lafiya a Afrika
2019-11-18 10:06:17        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yabawa kasar Sin saboda cigaba da tallafawa fannin kiwon lafiya a kasashen Afrika, musamman bisa yadda take kai daukin gaggawa da zarar an samu barkewar cutuka a nahiyar kamar annobar cutar Ebola.

Da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kwamishiniyar sashen kula da jin dadin jama'a ta AU, Amira Elfadil, ta ce kasar Sin tana cigaba da taimakawa AU musamman wajen samar da taimakon kudade da na kwararru ga cibiyar riga kafin yaduwar cutuka ta Afrika (Africa CDC).

Kwamishiniyar ta ce, kasar Sin tana tallafawa dukkan sassan da suka shafi kiwon lafiya, kuma ta fi mayar da hankali ne wajen karawa Afrika kaimi a fannin yaki da barkewar cutuka, musamman annoba, kuma tana ba da tallafin kudade da na kwararru.

Ta ce tallafin kudaden da kasar Sin ta samar ana amfani da su wajen gina dakunan gwaje gwaje, kuma wadannan dakunan gwaje gwajen wani bangare ne na aikin gina cibiyar riga kafin yaduwar cutuka ta Africa CDC a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, kuma aikin yana gudana yadda ya kamata.

A yayin da AU ke shirin gudanar taron koli game da cutar Ebola, inda ake sa ran neman taimakon kudade daga mambobin kasashen da sauran kungiyoyi don samar da kudaden da ake bukata don gudanar da aikin yaki da cutar Ebola da sauran cutuka masu yaduwa a nahiyar Afrika. Elfadil ta ce tuni gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin ba da gudunmowar dala miliyan guda. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China