Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bukaci Afrika ta karfafa gwiwa ga 'yan asalin nahiyar mazauna ketare wajen turo kudi ga nahiyar
2019-12-18 13:23:45        cri
Wani jami'in MDD ya bukaci gwamnatocin kasashen Afrika su bullo da wani tsarin da zai baiwa 'yan asalin nahiyar dake zaune a kasashen ketare kwarin gwiwa wajen turo kudinsu zuwa nahiyar.

Siddharth Chatterjeem, wakilin MDD dake kasar Kenya, ya fada a yayin wani taron dandalin 'yan asalin nahiyar mazauna ketare a Nairobi cewa, 'yan asalin kasashen Afrika dake zaune a ketare sun kasance jigon kawo sauye sauye ga cigaban tattalin arzikin nahiyar.

Chatterjee, ya bayyana a wajen taron 'yan kasar Kenya mazauna kasashen waje karo na 6 cewa, akwai bukatar samar da tsarin bada kwarin gwiwa ta hanyar saukaka kudaden haraji, da sayar da takardun lamuni na dogon lokaci, da daukar matakan rage hasara, domin 'yan Afrika mazauna ketare su zuba jarinsu a cikin nahiyar.

Taron na wuni uku, ya samu halartar 'yan kasar Kenya mazauna kasashe waje inda suka yi nazari game da hanyoyin da za su bayar da gudummowarsu wajen raya cigaban kasar.

Chatterjee ya lura cewa, tura kudi ya kasance muhimmin jigo game da musayar kudaden waje a kasashen Afrika da dama, kuma wasu lokutan ma yawan kudaden ya zarce wanda aka samu ta hanyar fitar da wasu kayayyakin cinikin da aka saba yi zuwa ketare, kamar su kofi, ganyen shayi, da furanni.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China