Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan kasar Sin: Kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afrika yaki da Cutar COVID-19
2020-03-18 11:58:07        cri

Jakadan kasar Sin a Kenya, Wu Peng, ya bayyana a jiya cewa, kasarsa zata bayyana gogewar da ta samu wajen yaki da cutar COVID-19 ga kasashen Afrika, tare da samar musu da tallafin kayayyaki iya karfinta.

Wu Peng ya ce gwamnatin kasar Sin ta samar da kayayyakin gwaji 10,000 ta hannun cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika. Kuma yanzu haka, Kenya ta samu wani adadi na kayayyakin, wadanda suka taka rawa wajen saukaka bukatarsu. Ya ce suna aiki da wasu kasashen nahiyar domin samar musu kayayyakin, yana mai cewa Kenya na cikin jerin kasashen, sai dai za a dauki wani lokaci.

Ya ce gwamnatin kasar Sin na iya bakin kokarinta wajen taimakawa nahiyar Afrika, yana mai cewa kamfanoni da al'ummar kasar ma na ba da taimakonsu, kuma wasu kamfanoni sun yi alkawarin samar da kayayyakin gwaji da na kariya ga kasar Kenya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China