Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani da dan jarida a Nijeriya sun jinjinawa ziyarar Wang Yi a Afrika
2020-01-13 13:56:42        cri

Wani masani dan Nijeriya ya zanta da manema labarai na CMG, inda ya dora muhimmanci sosai kan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai a nahiyar Afrika, wanda ta kasance ziyara ta farko da ya gudanar a sabuwar shekara, a ganinsu, hadin kan Sin da Afrika sun ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa na Afrika, da kuma cimma nasarar neman amfana juna da cin moriya tare.

Direktan sashin kula da dangantakar kasa da kasa da siyasa na jami'ar Abuja, dakta Sheriff Ghali Ibrahim ya nuna cewa, a cewar Wang Yi, layin dogo dake tsakanin Mambasa da Nairobi abin koyi ne kan hadin kan Sin da Afrika, abin da ke bayyana yadda hadin kai da Sin da Nijeriya suka yi a fannin layin dogo, hanyoyoin mota da tasoshin jiragen sama da dai sauransu, a ganinsa, Sin ta dade tana mutunta muradun kasashen nahiyar Afrika, da kuma samar musu taimako bisa bukatunsu da ciyar da bunkasuwar kasashen gaba.

Direktan kula da ka'idoji da dangantakar kasa da kasa na kafar yada labarai ta Nijeirya NAN Lawal Sale ya ce, ziyarar farko a sabuwar shekara da ministan harkokin wajen kasar Sin ya ke kaiwa kullum a nahiyar Afrika a cikin shekaru 30 da suka gabata, abin jinjinawa sosai, kuma yana sa ran Sin da Nijeriya da ma Afrika baki daya, za su kara habaka hadin kai a tsakaninsu don samun ci gaba tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China